28 Satumba 2020 - 11:03
Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ta Jaddada Anniyarta Ta Ci Gaba Da Neman Fasahar Nukliya Ta Zaman Lafiya

Ma’aikatar makamashin nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa za ta ci gaba da ayyukan bincike da kuma neman fasahar makamashin nukliya ta zaman lafiya a fagagen kiwon lafiya, ayyukan noma, da kuma magunguna.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) ta nakalto hukumar ta na fadar haka ne a cikin shafinta na Twitter a jiya Asabar, wacce ta yi dai-dai da ranar 26 ga watan Satumba, ranar da MDD ta ware don raya fasahar nukliya ta zaman lafiya a duniya.

Ma’aikatar ta kara da cewa a rana irin ta yau ne yakamata a sanar wa duniya kan cewa amfani da fasahar nukliya ta zaman lafiya da ci gaba, hakki ne na ko wace kasa a duniya, sannan a nunawa kasashe masu girman kai a duniya kan cewa ba hakkinsu ba ne su takaita wannan fasahar a tsakaninsu ba.

Kafin haka dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa HKI ce babbar barazana a yankin Asia ta kudu don makaman nukliyan da ta tara a yankin.

342/